Miliyoyin Isra'ilawa sun kada kuri'unsu

Image caption Ana gudanar da zabe a Isra'ila

Miliyoyin bani Isra'ila sun kada kuri'arsu a babban zaban da akai a kasar, inda Praminista, Benyamin Netanyahu, ke fatan sake yin nasarar samun wa'adi na uku.

Jami'ai sun ce kimanin kashi hamsun cikin dari na masu kada kuri'a sun fito, wanda wani babban ci gaba ne idan aka kwatanta da zaban da akai shekaru ukun da su ka wuce.

Sakamakon jin ra'ayin jama'a ya nuna jam'iyyar gamayya ta masu ra'ayin rikau ta Mr Netanyahu za ta yi nasara, amma kujerun da take dasu a majalisa za su ragu.

Sakamakon jin ra'ayin jama'ar na nuna cewa a 'yan kwanakinnan babbar jam'iyyar adawa ta Bait Yehudi mai tsatsatsauran ra'ayin rikau na samun galaba akan jam'iyyar gamayya dake mulki a Isra'ila.

Karin bayani