An hana Acaba a Kano

Wasu masu babura
Image caption Dama can akwai dokar takaita zirga-zirgan babura a jihar ta Kano

Gwamnatin jihar Kano dake arewacin Najeriya ta fitar da wata sabuwar doka da ta hana sana'ar acaba a jihar.

A wata sanarwar da gwamnatin ta bayar, ta ce dokar wadda ta hana mutane biyu hawa babur, za ta fara aiki ne a ranar Alhamis mai zuwa.

Hakan dai a cewar gwamnatin, ya biyo bayan amfani da baburan da ake yi wajen kai hare-hare a sassan birnin.

Jihar ta Kano na fuskantar matsalar tsaro, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da jami'an tsaro.

A karshen makon da ya gabata ne, wasu mahara suka kai hari kan tawagar sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, inda direbansa da wani cikin dogaransa suka rasa rayukansu.

Wata kididdiga ta nuna cewa, jihar na da kimanin masu baburan haya sama da miliyan biyu, kuma an shafe shekaru da dama ana amfani da baburan haya a matsayin hanyar sufuri a jihar da ta fi kowa yawan jama'a a Najeriya.

Tuni jihohi da dama da kuma babban birnin tarayyar Najeriyar Abuja, suka hana sana'ar acabar.

A lokuta da dama masu sana'ar na cewa, ana daukar irin wadannan matakan ne ba tare da an tanadar musu wata sana'ar ba, ko kuma samar musu hanyar da za su rinka ciyar da iyalansu.