An kashe akalla mutane 18 a garin Damboa

'Yan sandan Najeriya
Image caption An kashe mutane a kasuwar Damnboa

Jami'ai a Najeriya sun ce akalla mutane 18 ne wasu da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne su ka kashe a garin Dambuwa dake jahar Borno.

Jami'ai sun ce an kai hari ne ranar Litinin da yamma kan mafarauta sabili da su na sayar da naman biri da mugun dawa da ma wasu namun dajin, wadanda aka haramtawa musulmai ci.

Kungiyar Boko haram--- wadda ke san tilasta amfani da shari'ar musulunci-- na kai hare-hare a Najeriya, musamman a arewaci kasar.

Wani labarin kuma na cewa tun da farko mafarautan sun taimakawa sojoji gano wani dan kungiyar Boko Harm din, dan haka harin na ranar Litinin kamar wani ramuwar gayya ne.

Fiye da mutane 600 ne aka kashe bara a hare-haren da kungiyar ta kai a fadin kasar.

Karin bayani