Nijar na shirin tura sojoji 500 Mali

Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou
Image caption Wasu kasashen yammacin Afrika kamar Najeriya tuni suka tura nasu sojojin Mali

A yau ne shugaban jamhuriyyar Nijar, Alhaji Mahamadou Issoufou ya ziyarci ayarin sojojin kasar da za a tura Mali.

Shugaban kasar ya je ne domin ganin yanayin da sojojin ke ciki, tare da kara musu kwarin guiwa game da nauyin da kasa ta dora musu.

Sojojin sun kafa sansaninsu ne a Walam, kimanin kilomita 100 a arewacin Yamai, babban birnin kasar, inda suke shirye-shiryen tafiya.

Ko da yake har yanzu ba a bayyana ranar da za su tashi zuwa Malin ba.

Nijar za ta tura sojoji 500 cikin shirin kungiyar ECOWAS, domin taimaka wa gwamnatin Mali wajen kwato yankin arewacin kasar da ke hannun 'yan tawaye tun farkon shekarar da ta gabata.