Obama zai bunkasa tattalin arzikin Amurka

Image caption Obama ya yi rantsuwar wa'adi na biyu

Shugaba Obama ya kaddamar da wa'adin mulkinsa na biyu da jawabin alkawarin farfado da tattalin arziki da kuma kawo karshen tsoma kasar cikin yaki.

Lokacin da yake jawabi ga daruruwan dubban mutane a dandalin taro na kasa dake birnin Washington, Shugaba Obaman yace Amurkawa a koda yaushe suna da fahimtar cewa lallai ne su fuskanci sabbin kalubale.

Mr Obama ya ci alwashin farfado da tattalin arziki ta kowa ne hali da kuma kokarin kawo karshen yake yake.

Amurkar dai na fuskantar kalubale sosai wajan zabin hanyoyin da za a bi na cike gurbin kasafin kudi.

Shugaba Obama ya ce tsarin harkokin waje na da batutwa biyu zaman lafiya da tsaro wanda ba wai sai an kai ga shiga filin daga ba, amma inji Shugaban kasar, Amurka za ta kasance mai kazar kazar da kuma lura ga duk wanda zai cutar da ita.

Magoya bayan Obama dai na ganin wannan karon mulkin sa zai sake sauyawa yadda za ayi abubuwan mamaki da ba a taba zata zai yi su ba.

Karin bayani