An fara sauraron karar Charles Taylor

Charles Taylor
Image caption Kimanin mutane dubu 50 ne suka rasa rayukansu a yakin basasar na Saliyo

Wata kotun Saliyo dake Hague, ta fara sauraron karar da tsohon shugaban kasar Liberia, Charles Taylor ya daukaka game da hukuncin daurin da aka yi masa.

A watan Mayun shekarar da ta gabata ne, kotun ta musamman ta yanke wa mista Taylor shekaru 50 a gidan kaso, bayan ta same shi da laifin tallafa wa 'yan tawaye a yakin basasar da aka yi a Saliyo a shekarun 1991 zuwa 2002.

Masu kare wanda ake kara sun bayyana hukuncin da cewa "Rashin adalci ne", inda suka nemi a rushe hukuncin.

A waje daya kuma rahotanni sun nuna cewa Taylor ya rubuta wa majalisar kasarsa takarda na neman kudaden fanshon shugaban kasar da suka kai dalar Amurka dubu 25.

Yana mai bayyana rike kudaden fanshonsa a matsayin babban rashin adalci.

Haka kuma an ambato Mista Taylor ya ce, an tauye masa hurumin yin hurda da ofishin jakadancin Liberia a Hague, tare da sauran hidimomi na diplomasiyya, a matsayinsa na tsohon shugaban kasa.

Charles Taylor ne tsohon shugaban kasan Afrika na farko da aka taba samu da laifin aikata manyan laifukan yaki, tun bayan shari'ar Nuremberg na Nazis, bayan yakin duniya na biyu.

A tsawon lokacin shari'ar dai, Taylor ya hakikance cewa bai aikata laifin ba.