'Kuri'ar raba-gardamar makomar Burtaniya a Tarayyar Turai'

Fira Ministan Burtaniya David Cameron
Image caption Burtaniya na nazari kan zamanta a Tarayyar Turai

Fira Ministan Burtaniya David Cameron ya yi kiran a gudanar da kuri'ar raba-gardama kan makomar kasar a Tarayyar Turai.

A lokacin wani jawabi da aka dade na dako, Mr Cameron ya ce za a kada kuri'ar ne kan ci gaba da zama a kungiyar ko kuma a'a, a shekara ta 2018, idan har jam'iyyarsa ta Conservative ta sake lashe zabe.

Sai dai ya ce hakan zai biyo tattaunawar da za a yi ne kan sake duba matsayin Burtaniya a kungiyar

Mr Cameron ya kara da cewa akwai babban gibi tsakanin Tarayyar Turai da kuma jama'arta, wanda ake jin tasirinsa matuka a Burtaniya.

An soma maida martani

Tuni aka fara mayar da martani ga jawabin na Mr. Cameron, inda ministan harkokin wajen Faransa Lauren Fabus, ya ce shirin na da matukar hadari.

Ya kara da cewa wajibi ne mambobin kungiyar su yi aiki da ka'idojinta.

Shima ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, ya ce zama a kungiyar zabi daya ne wato ciki ko waje, yana mai cewa kogo-bo-kon baya ba mafita ba ce.

Shi kuwa Jakadan Finland a Burtaniya cewa ya yi kasarsa ba za ta so Burtaniya ta fice daga Tarayyar Turai ba.

Karin bayani