Kasashen Turai sun maida martani kan shirin Burtaniya

David Cameron
Image caption Burtaniya na nazari kan zamanta a Tarayyar Turai

Kasashen Turai na ci gaba da mayar da martani ga shirin Burtaniya na gudanar da kuri'ar raba-gardama kan makomarta a kungiyar Tarayyar Turai.

Fira minista David Cameron, ya ce yana son Burtaniya ta ci gaba da zama a kungiyar a lokacin yake sake tattaunawa kan dangantakar kasar da Turan, sannan a gudanar da zaben raba-gardama kan sabbin yarjeniyoyin a shekara ta 2018 idan aka sake zaben jam'iyyarsa.

Shugabar Jamus Angela Merkel, ta ce a shirya kasarta take ta tattauna kan bukatun Burtaniya, amma sai an samo matsayar da dukkan kasashe za su amince da ita.

Ita ma hukumar tarayyar Turai a birnin Brussels ta ce yana da matukar muhimmanci ga Tarayyar da kuma Burtaniyar, ta ci gaba da kasancewa cikakkiyar mamba a Tarayyar.

Karin bayani