Hillary Clinton ta dauki alhakin harin Benghazi

Hillary Clinton
Image caption Hillary Clinton ta yi karin haske kan harin Benghazi

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta bayyana harin da aka kai birnin Benghazi na Libya wanda yayi sanadiyyar kisan jakadan Amurka a kasar, da cewa wani bangare ne na kalubalan da manufofin Amurkar ke fuskanta a arewacin Afrika.

Da take bayar da bahasi ga kwamitin kula da harkokin wajen na majalisar Dattawan kasar, Mrs Clinton ta ce ta dauki alhakin lamarin.

Mrs Clinton tace ''kamar yadda na sha nanata wa, na dauki alhakin abinda ya faru, kuma babu wanda ya fi ni son ganin abubuwa sun tafi daidai''.

Tuni dai aka kori wasu ma'aikata uku a ofishin kula da harkokin wajen su uku saboda gazawa wurin samar da tsaro a birnin na Benghazi.