An sami bullar cutar polio a Masar

Mohmmed Morsi na Masar
Image caption Za a gudanar da shirin yaki da cutar polio a Masar

Hukumomi a kasar Masar sun ce za su gudanar da allurar rigakafin cutar shan inna ta Polio bayan da aka gano nau'in cutar a wata shara a birnin Alkahira.

Babu wanda ya nuna alamar kamuwa da cutar kawo yanzu, rabon da a samu cutar Polio a kasar ta Masar tun shekara ta 2004.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce kwayoyin cutar sun yi kama da wadanda aka gano a Kudancin Pakistan.

A kwanakin baya an samu tsaiko a yunkurin da ake na kawar da cutar a Pakistan bayan da aka kashe mutane tara da ke aikin alluarar rigakafin cikin mako guda.

Ana matukar kokarin gananin an kawar da cutar daga cikin kasashen ukun da har yanzu ke fama da ita, wato Afghanistan da Najeriya da kuma Pakistan.

Karin bayani