Kungiyoyin agaji za su yi gangami kan yunwa

Yara masu fama da yunwa
Image caption Yara masu fama da yunwa

Kungiyoyin agaji na kasa da kasa fiye da dari za su hadu domin kaddamar da gangamin kawar da yunwa, musamman a kasashe masu tasowa.

Wannan shi ne hadin gwiwa mafi girma da kungiyoyin za su yi tun bayan gangamin kawar da talauci da aka yi a shekarar 2005.

Za'a kaddamar da shi ne a daidai lokacin da Birtaniya za ta karbi shugabancin kungiyar kasashen duniya masu karfin tattalin arziki watau G8 a bana.

Game da batun kaddamar da gangamin kawar da yunwar da za a kaddamar, shugaban kungiyar agaji ta 'Save the Children' Justin Forsed ya ce wadanda suka shirya gangamin basu yi nasara ba wajen kawar da talauci a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Sai dai Mr Justin din ya cesun kawo sauyi, saboda sun kubutar da miliyoyim mutane daga kangin talauci.

Ya kuma kara da cewa kalubalen dake gaban ci gaban da aka samu shine yunwa.

Sabon gangamin zai maida hankali kan ganin kasashen duniya masu karfin tattalin arziki, sun cika alkawuran samar da tallafi tare da samar da karin tallafi ga manoma.

Gangamin zai kuma matsawa kamfanonin duniya biyan haraji a kasashe masu tasowa.