Netanyahu zai kafa gwamnatin kawance

Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Image caption Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya kudiri aniyar kafa gwamnatin kawancen da zata kunshi jam'iyu daban-daban a kasar.

Wannan ya biyo bayan nasarar da jam'iyarsa ta kawance, Likud-Beitenu ta samu a babban zaben da aka gudanar.

Sai dai kuma jam'iyar ta rasa rubu'in kujerunta ta a Majalisa dokokin kasar.

Sabuwar jam'iyar Yesh Atid, wacce tsohon mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin, Yair Lapid ke jagoranta ce ake sa ran zata zama jam'iya ta biyu mafi rinjaye a majalisar dokokin kasar.

An kuma bayyana cewa ita ma jam'iyar Bayit Yehudi ta samu karin nasarori.

Yayinda yake gabatar da jawaban samun galaba, Mr Netanyawu ya ce kalubalen dake gaban sabuwar gwamnatinsa shine hana kasar Iran mallakar makaman nuclear.

Mr Netanyahun ya yi amannar cewa sakamakon zaben zai sake bashi wata dama ta kawo sauyi kan abinda 'yan kasar ta Isra'ila ke bukata.