Mahara sun yanka mutane a Maiduguri

Shingen binciken ababen hawa
Image caption Maiduguri ta kwashe shekaru tana fuskantar matsalar tsaro, halin da ya kai ga mutuwar mutane da dama

Rahotanni daga Najeriya na cewa wadansu mutane da ba a san ko su wanene ba, sun kai hari a Maduguri dake jihar Borno, inda suka yanka mutane biyar.

Mazauna birnin sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da daddare, kuma tuni jami'an tsaro suka kwashe gawawwakin.

Maharan sun haura wani gida a unguwar Jiddadri Polo, inda suka kashe maigidan da dansa, kana suka kashe karin mutane uku a wadansu gidajen, kamar yadda wani ganau ya shaida wa BBC.

A wata sanarwa da kakakin rundunar tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno, JTF ta fitar, wanda Laftanal Kanal Sagir Musa ya sanya wa hannu, ta ce mutane uku 'yan bindigan suka kashe.

A cewar JTF, bayan kisan ne aka sanar da jami'anta, wadanda suka je unguwar, inda suka yi bata-kashi tsakaninsu da 'yan bindigar.

Lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar 'yan bindigan biyu tare da raunata wani jami'in soji.

JTF ta kara da cewa jami'ansu sun kama mutane uku da suke zargi da kisan, sannan sun samu bindiga da alburusai a hannunsu.