Satar mutane na karuwa a Kamaru

Image caption Paul Biya, shugaban Kamaru

Hukumomi a Kamaru sun fara nazarin hanyoyin da zasu bi domin shawo kan bala'in yawan sace mutane ana kashe su da nufin yin tsafi a birnin Yaounde.

Wannan al'amarin ya fara ne tun wasu 'yan watannin baya a unguwar Mimboman da take a kudancin babban birnin Yaounden, inda cikin kwanaki 2 zuwa 3 akan tadda gawawwakin mutane masamman ma 'yan mata a cikin jeji.

Hukumomin sun dauki mataki na farko na kafa barikin 'yan sanda a wannan unguwar, wadanda zasu rika yin aikin sintiri, da kuma gudanar da bincike domin gano masabbabin abinda yake haddasa irin wannan aika-aikar.

Tuni dai ministan sadarwa na Kamarun ya ce gwamnati da jami'an tsaro sun soma bincike akan wannan lamari.