Burtaniya za ta ci gaba da tallafawa Najeriya

Firayim Ministan Burtaniya David Cameron
Image caption Firayim Ministan Burtaniya David Cameron

Burtaniya ta ce za ta ci gaba da tallafawa Najeriya, duk da shirin tsuke bakin aljihun da ta ke yi a karkashin jagorancin Firaminista David Cameron.

Jakadan kasar ta Burtaniya a Najeriya, Mista Andrew Pocock, ya shaidawa BBC cewa Burtaniyar na wani shiri na karfafa jami'an tsaron Najeriyar, da kuma inganta rayuwar jama'a.

Tabbatar da tsaro in ji jakadan, na daya daga cikin abubuwan da Burtaniyar ke tallafawa Najeriyar, tana kuma kai dauki ta fuska biyu.

Jakada Andrew ya ce da farko suna aiki da gwamnatocin jihohi da na tarayya don ganin yadda za a tallafa wajen karfafa jami'an tsaro.

Ya kuma ce wani abu mai muhimmanci shine kokarin kawar da abubuwan dake haifar da takaddama kamar talauci, rashin adalci da sauransu, musamman a arewacin kasar, inda ake kokarin magance zaman kashe wando, ilmi, kula da lafiya da makamantansu.

Kimanin fan miliyan dari uku ne Burtaniyar ke kashewa wajen tallafi a Najeriya a ko wace shekara, don kara inganta rayuwar jama'a.

Sai dai 'yan kasar da dama na cewa ba kasafai wannan tallafi ke zuwa garesu ba.