Amurka ta tuhumi wasu mutane 3 da kirkirar kwayar cutar Kwamfuta

Kwayar cutar Kwamfuta
Image caption Kwayar cutar Kwamfuta

Hukumomin Amurka sun tuhumi wasu mutane uku da laifin kirkira da yada wata kwayar cutar kwamfuta, mafi haddasa asara da aka taba gani.

Kwararru sun ce tana daya daga cikin nau'in kwayoyin cutar kwamfuta da suka fi haddasa asara ta fannin kudi da aka taba gani.

Kwayar cutar ta kwanfuta mai suna Gozi, ta shafi kwamfutoci sama da miliyan daya a fadin duniya, daga 2005 har zuwa watan Maris na 2012.

Mutanen ukun da ake tuhumasun hada da dan kasar Rasha, Latvia da kuma Romania.

Mai gabatar da karar a birnin Manhattan, inda aka gurfanar da mutanen ya ce sun gudanar da sabuwar hanyar fashi ta zamani da ba a bukatar bindiga ko takunkumin fuska na badda kama.

Ya kuma shaidawa kotun da aka gurfanar da mutanen uku da dukkanninsu suke tsakanin shekaru 20 cewa, sun yi amfani da fasahar ne wajen samun bayanan asusun bankuna na jama'a inda aka sace dubban miliyoyin daloli.

Dan kasar Rashan mai suna Nikita Kuzmin, ya kirkiro kwayar cutar kwamfutar da shi da sauran abokanan ta'asar ta sa biyu, su ka watsa kwayar cutar a kasashen Turai da Amurka tsakanin 2005 zuwa watan Maris na 2012.

Ta shafi kwamfutoci da yawa

Kwayar cutar kwamfutar da suka kirkira, ta shafi sama da kwamfutoci miliyan daya a fadin duniya, har ma da na hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka, NASA.

Mai gabatar da karar ya ce, ta wannan hanya suka rika yaudarar dubban masu ajiya a bankuna, suna basu bayanansu na ajiya a banki, inda daga bisani su ke amfani da hakan wajen kwashe wa musu dubban miliyoyin daloli don azurta kansu, da kuma wasu mutanen da suka saidawa wannan muguwar fasaha.

A binciken da gwamnatin Amurka ke yi a yanzu ta yi zargin cewa an fara aiwatar da ta'asar ne a kasashen Turai, daga nan aka yada zuwa Amurka inda a lokaci daya aka yada cutar a kwamfutocin Hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka NASA sama da 160.

Hukumar binciken laifuka ta tarayya ta Amurka FBI ta yi aiki da hadin guiwar Burtania, Finland, Netherlands, Latvia, Moldova, Romania da kuma Switzerland wajen bankado hanyar zambar.