Sojojin Mali na kashe-kashen ba gaira ba dalili

Sojojin Faransa a birnin Savare, kasar Mali
Image caption Sojojin Faransa a birnin Savare, kasar Mali

Wata kungiyar kare hakkin biladama ta kasa da kasa, ta yi Allah wadai da abinda ta kira kisan babu gaira babu dalili da sojojin kasar Mali ke yi.

Kungiyar mai suna International Federation of Human Rights dake birnin Paris, ta ce makwanni biyun da suka gabata rundunar sojin ta Mali ta aikata irin wadannan kashe-kashen a wasu garuruwa biyu dake tsakiyar kasar.

Ta ce Sojojin na aikata hakan ne yayinda suke artabu da mayaka 'yan tawaye, da taimakon dakarun kasar Faransa.

Kungiyar ta ce akwai kashe-kashe kimanin talatin da sojojin suka aikata a garin Sevare, da kuma wani garin dake kusa a cikin makonnin biyun da suka gabata.

Ta ce a cikin sa'oi ashirin da hudu, dakarun gwamnatin kasar ta Mali, sun hana akasarin manema labaran kasashen waje isa zuwa cikin garin na Sevare.

Kungiyar kare hakkin biladaman ta kuma jaddada cewa wannan zargi wani babban abin kunya ne ga kasar Faransa , wacce ke marawa dakarun kasar ta Mali baya.

Ministan harkokin tsaron Faransa Jean Yves Le Drian, ya ce dole jami'an sojin kasar Mali su tabbatar da cewa sun kiyaye cin zarafin jama'a.

Wasu rahotanni na nuna cewa akasari dakarun kasar Mali bakaken fata ne ke far wa Larabawa, da Abzinawan dake arewacin kasar, da ake zargi da marawa mayaka 'yan tawayen baya.

Wannan ya bankado wani bangare na yakin dake nuna wariyar launin fata.