'Yan gudun hijira daga Syria zuwa Jordan sun karu

Syria
Image caption Ana kara samun matsalar 'yan gudun hijira

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Jordan ya bayyana kamarin matsalar 'yan gudun hijira daga Syria a kasar Jordan.

Jagoran kula na ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Jordan, Andrew Harper, ya fadi yawan 'yan gudun hijirar da ke shiga Jordan din daga Syria.

Andrewa Harper ya ce "Lalle abin ya yi tsanani, muna karbar mutane daga dubu biyu zuwa dubu uku kowane dare, mun san akwai kamar dubu hamsin zuwa sittin da ke son ketaro kan iyaka su shigo Jordan."

'Yan gudun hijira fiye da dubu ashirin da biyar be suka isa Jordan tun da aka shiga sabuwar shekarar da ake ciki.

Karin bayani