Amurka za ta kyale mata suna shiga fagen daga

Sakataren Harkokin Tsaron Amurka, Leon Panetta
Image caption Sakataren Harkokin Tsaron Amurka, Leon Panetta

A karo na farko, rundunar sojin Amurka za ta rika kyale mata suna shiga don a fafata da su a fagen daga.

Nan gaba a yau ne Sakataren Tsaron Amurkar, Leon Panetta, zai ba da sanarwar wannan sauyi, wanda zai kawo karshen wata doka da aka kafa shekaru ashirin da suka wuce.

Sauyin zai kuma bude guraben ayyuka dubu dari biyu da hamsin na fagen daga da na sojin kundumbala ga mata.

A shekarar da ta gabata aka fara yin sassauci a kan dokar, lokacin da aka kyale mata su yi ayyukan da ke da alaka da fagen daga.

Sai dai kuma kwamandojin kasar, za su ci gaba da fayyace ayyukan da a ganinsu ba za a bar mata su gudanar ba.