Farfado da noman auduga a Najeriya

Wani manomi a Najeriya
Image caption Wani manomi a Najeriya

Yayin da Najeriya ke ci gaba da fama da matsalolin tattalin arziki, wasu gwamnatocin arewacin kasar na ganin farfado da harkar noma shi ne zabi.

Daya daga cikin amfanin gona da gwamnatocin suka dauki matakin inganta nomawa ita ce auduga.

A baya dai gwamnatoci sun sha bullo da shirye-shirye da sunan inganta noma amma abin ya faskara, koda yake mahukunta na cewa wannan karon ba da wasa suke ba.

Jihohin arewacin Najeriyar dake kokarin bunkasa noman na auduga tare da tallafin gwamnatin tarayya dai, sun bayyana cewa wannan mataki ya zamo wajibi domin kauce wa dogaro kan kudaden albarkatun man petur da ake hakowa a jihohin kudancin kasar.

To sai dai kuma duk da cewa manoman audugar sun yi marhabun da shirin, har yanzu suna fuskantar matsaloli ta fuskar ganin darajar audugar kanta.

Ko baya ga haka manoman na auduga na kokakawa da rashin samun kayan aikin noma a cikin lokaci kuma a wadace.

A shekarun baya dai noman da arewacin Najeriya ya shahara a kai, ya kasance kashin bayan tattalin arzikin kasar, kafin a yi watsi da shi a rungumi albarkatun man petur.