Twitter: An dakatar da shafin Al Shabaab

Image caption Shafin Al Shabaab da aka dakatar

An dakatar da shafin Twitter na ƙungiyar 'yan takifen Somalia ta Al-Shabab bayan da suka yi amfani da shafin wajen yin barazanar hallaka yan ƙasar Kenya da suka yi garkuwa da su.

Kamfanin na Twitter ya ki cewa komai akan dakatar da shafin, ko da yake dokokinsa ya haramta sanya barazanar haddasa tarzoma.

A ranar laraba ƙungiyar Islamar ta bayyana cewa rayuwar 'yan Kenyar da ta yi garkuwa da su na cikin hadari idan har Kenya ba ta sako fursunonin siyasar da take riƙe da su.

Tun da farko a wannan watan Al-Shabab ta sanar a shafinta na Twitter cewa za ta kashe wani bafaranshe Denis Alexx wanda ta yi garkuwa da shi ta kuma aikata hakan daga bisani.

Sai dai gwamnatin Faransa ta ce ya rasa ransa ne a lokacin da aka yi kokarin ceto shi makonni biyu da suka wuce.