Bikin aure ya koma zaman makoki

Rahotanni daga jahar Taraba da ke arewa masu gabashin Najeriya na cewa an yiwa wani ango yankan rago a lokacin da ake shagulgullan bikin aurensa a kauyen Tunga Rugere da ke karamar hukumar Sardauna.

Bayan aukuwar lamarin a daren juma'a, an kai gawar angon garin Goje inda aka wuce da ita zuwa Gyambu.

Rahotanni sun ce lamarin ya daru ne a cikin duhu bayan da wasu wadanda ba a san ko su wanene ba suka tsayar da janaretan da ke bada hasken wutar lantarki a wurin da ake gudanar da hidimar bikin auren.

Jama'ar da ke wurin sun ce sun ga wasu mutane biyu da fito da wuka tare da yi wa angon mai suna Ado wanda makanike ne yankan rago.