An kashe mutane akalla hamsin a Venezuela

Zanga-zanga a gidan yari, Venezuela
Image caption Zanga-zanga a gidan yari, Venezuela

Ma'aikatan asibiti a Venezuela sun ce an kashe mutane hamsin, da kuma jikkata wasu, yayin wata tarzoma a gidan yari dake birnin Barquisimeto a yammacin kasar.

Minista mai kula da gidajen yari, Iris Varela, ta ce an aike da sojoji gidan yarin don su bincika ko akwai makamai.

Ta kara da cewa labarin binciken da kafofin yada labarai suka bayar ne ya haddasa tarzomar.

Akasarin wadanda suka yi rauni dai harbinsu aka yi da bindiga; wadanda suka mutu kuma sun hada da fursunoni da gandurobobi da ma'aikatan gidan yari.

Yawan fursunoni a gidajen yarin Venezuela ya ninka adadin da ya kamata su dauka har sau uku.