Zaman dar-dar a jihar Plateau

Rahotanni daga jihar Filaton Nijeriya na cewa an kwana cikin zaman dar-dar a Jos babban birnin jihar sakamakon matakin da gwamnatin jihar ta dauka na rusa gidaje da wasu gine-gine na mutane da talatainin dare.

Jama'a dai sun fito cikin daren suka nuna rashin amincewarsu da matakin na gwamnati na rusa gine-ginen wadanda ta ce an yi su ba bisa ka'ida ba.

Wasu da lamarin ya shafa kuma na cewa suna da takardunsu.

Kasancewar unguwar da gwamnatin jihar ta Filato ta kuduri aniyar rusawa da m sauran unguwananni dake kewaye da ita galibin mazaunansu musulmi, nan da nan sai daruruwan musulmi suka fito cikin daren suna kabbara.

A kwanakin baya dai gwamnatin jihar ta Filato ta rusa gidaje da dama a unguwar da ma wasu unguwanni a cikin birnin na Jos da rana, lamarin daya nemi janyo rigima kuma tana zargin cewa gine-ginen basa bisa ka'ida ne saboi da babu takardu kum ababu izini, amma wasu daga cikin wadanda lamarin ya shafi gine-ginensu, sun musanta wannan zargi suna masu cewa suna da takardunsu cif-cif.

Kwamshinan gidaje da raya birane na jihar Filato, Mista Solomon Maren, ya ce ba su je da niyyar rusa gidajen da mutane ke ciki ba domin su masu tausayi ne, gidajen da suka shirin rudsawa da daren su ne wadabnda ba a kammala ba, kuma sun dauki matakin rusa wurane da dare ne domin kada lamarin ya kawo cikas ga harkokin jama'a da rana.

Kwamishian ya kuma musanta nuna bambancin bangare a aikin.

Jihar ta Filato dai ta sha fama rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa inda dubban mutane suka rasa rayukansu kuma matakin na rusa gidaje na zuwa yayin da jama'ar birnin na Jos ke kokarin murmurewa daga radadin irin wadannan tashe-tashen hankula, inda masharhanta ke cewa ganin halin da aka shiga matsayar ba a yi taka-tsantsan ba to matakin ka iya fama wannan daddaden gyambo.