Mexico: Yan sanda na neman mawaka

'Yan sanda arewacin Mexicon sun ce suna binciken wasu gungun mawaka da suka bace.

Su dai mawakan da akewa lakabi da Kombo Kolombia su goma sha biyu tare da wasu abokan aikinsu su takwas, sun bace ne bayan da suka kammala wake wake a garin Hidalgo a daren alhamis.

Wasu daga cikin iyalan mawakan sun shaidawa jami'an 'yan sanda cewa sun shiga cikin wani yanayi na damuwa ne bayan da mawakan suka daina amsa wayoyin salularsu.

Wakilin BBC yace a lokacin da 'yan uwan mawakan suka isa garin Hidalgo a jihar Nuevo Leon, in da mawakan suka yi wasa sun taradda da motocinsu amma babu kowa a ciki.