'Chavez ya bada hakuri cikin wata wasika'

Chavez
Image caption Chavez na fama da rashin lafiya

Mataimakin shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro, ya karanta wata wasika da yace shugaban kasar wanda ke fama da rashin lafiya Hugo Chavez ne ya rubuta.

Makonni kusan bakwai kenan ba a ga shugaban a filin ba tun lokacin da aka yi masa tiyata kan cutar daji.

Mr. Maduro ya karanta wasikar ce wacce aka sanya wa hannu da jan biro a wurin taron shugabannin yankin a kasar Chile.

Wasikar ta ce shugaba Chavez yana bayar da hakuri saboda bai samu damar halartar taron ba saboda ya na fama da rashin lafiya.

Sannan ya yi kira ga a samu hadin kai tsakanin kasashen Latin Amurka.

Karin bayani