An ci gaba da zanga zanga a Masar

An ci gaba da zanga-zanga a cikin dare a kasar Masar duk da dokar takaita zurga zurga da shugaba Muhammed Morsi ya sanya a ranar Lahadin da ta gabata.

Masu zanga-zangar sun yi maci ne a biranen Port Said da Ismailiya da kuma Suez a cikin dare duk da dokar tabacin da aka sa a biranen.

An kashe mutane da dama a zanga zangar da aka dauki kusan kwanaki biyar ana gudanarwa kenan.

Sai dai kuma Gamayyar Jam'iyun adawa ta kasar ta yi watsi da kiran da Shugaba Muhammad Morsi yayi na neman su halartarci wani taro domin tattaunawa a kan rikicin da kasar ke fuskanta.

Zanga zangar baya-bayan ta taso ne saboda hukuncin kisa da aka yankewa wasu mutane 21 bayan an same su da laifi a mutuwar wasu masoya kwallon kafa a Birnin Port Said kusan shekara daya da ta wuce.

Yawan mutanen da su ka mutu a zanga zangar na karuwa, inda ake ganin kusan mutane 50 ne zuwa 60 suka rasa rayukansu a arangamar da aka yi da jami'an tsaron a lokacin da aka fara gudanar da zanga zanga a ranar alhamis din da ta gabata ya zuwa yanzu.