Hangen rayuwa ta gaba a duniyar ka

Hangen rayuwa ta gaba
Image caption Ko me zai faru a rayuwa ta gaba? Idan a kaddara tunaninka zai iya bayyana abin da zai farun?

A kaddara kana iya hango gaba, ba mu labarin abin da ka gani ta hanyar zayyana hoton makoma ko yadda rayuwarmu ta gaba za ta kasance!

Kana iya amfani da hikimar zane da Komfuta, ko hoton kamara, ko zanen hannu ko kuma majigi wajen tura mana abin da ka hanga.

Kana iya yin wannan ta yadda kake so, wato wajen hangen rayuwa ta gaba a duniyar dake kewaye da kai, wanda ka iya kasancewa cikin gidanka ne ko waje.

Haka kuma yana iya zama yadda siga ko siffofinmu za su kasance, ko abincinmu ko kuma mu'amalarmu da juna, da yadda za mu dinga tafiye-tafiye ko gudanar da ayyukanmu, har ma da yadda duniyar za ta kasance, da kuma abubuwan da ake bukatar kirkira da na kaucewa da kuma wadanda za a kara inganta su.

Muna bukatar gangariyar ayyuka irin na kirkira, wadanda ka san ya kamata duniya ta san da su.

Za mu zabi ayyukan da suka kayatar.

Kuma an zabi alkalai biyar ta hanyar dauko kowane guda a cikinsu daga kowace nahiya ta duniya.

Alkalan za su darje wadanda suka shiga gasar wajen duba bajintarsu ta fannin kirkire-kirkire, da tasirin hotunansu da gangariyar abin da suka gina tunaninsu a kansa, da yadda ya kayatar da kuma girman sakon da hotunan ke isarwa.

Bangarorin gasar

An kasa gasar zuwa gida biyu, wato na hotunan kamara ko zanen hannu da kuma hotuna masu motsi wato bidiyo, kuma za a zabo zakara daya daga kowane bangare.

Akwai kyautar komfuta ko na'ura mai amfani da kwakwalwa da za a ba wa kowanne daga cikin mutum biyu da suka yi nasara, wadda kudinta ya kai fam dubu biyu da dari biyar, ko dala dubu uku da dari tara.

Za ku iya turo sakonninku ta wannan adireshin email din whatif@bbc.co.uk

Kuma bangare daya za ka iya shiga a gasar.

Za a rufe karbar sakonninku ne a ranar 8 ga watan maris na wannan shekarar da misalin karfe goma agogon GMT.

Ku sani cewa BBC za ta iya sarrafa hotunan da za ku turo yadda take so ba tare da wani sharadi ba.

Domin karin bayani kana iya shiga wannan shafin- bbc.co.uk/whatif ko whatif@bbc.co.uk