An yi alkawarin bada miliyan $455 kan Mali

Sojojin Faransa da aka tura Mali
Image caption Sojojin Faransa da aka tura Mali

Masu bada tallafi na kasa da kasa dake taro a Habasha, sun yi alkawarin bada dalar Amurka miliyan 455 domin magance batun masu fafutukar Islama a Mali.

Kudaden dai za a yi amfani da su wajen ayyukan agaji da kuma na dakarun hadin guiwa na Africa, Afisma da zasu karbi sojojin Faransa a kasar ta Mali.

Sai dai kudaden da aka yi alkawarin basu kai rabin abin da shugabannin Afrika suka bukata ba.

Sojojin Faransa da na Mali na tabbatar da tsaro a Timbuktu, bayan sun karbe iko da birnin a ranar Litinin.

Inda kuma hankalinsu yanzu ya karkata kan garin da masu fafutukar suka fi karfi wato Kidal.

Hakan na zuwa ne yayin da Birtaniya ta amince ta tura sojoji 350 Mali da kuma yammacin Afrika domin taimakawa sojojin Faransa.

40 cikin sojojin za su bada horo ne ga sojojin Mali, yayin da 200 kuma za a tura su wasu kasashen yammacin Afrika, inda can ma za su bada horo ne.