Sojojin Faransa, Mali na sintiri a Timbuktu

Sojojin Faransa tare da na Mali sun kwace garin Timbuktu mai dauke da dimbin tarihi daga 'yan tawaye masu kaifin kishin Islama a arewacin Malin.

Rahotanni sun ce sojojin sun shiga garin ne ba tare da fuskantar turjiya ba daga 'yan tawayen.

Kwamandojin sojin Faransa sunce a yanzu haka sojoji na sintiri a tintunan garin domin fatattakar sauran 'yan tawayen da su ka rage.

Muddin aka samu kyakyawan tsaro a garin na Timbuktu, sojojin za su maida hankali ne a gari na karshe da yan tawayen ke da karfi wato Kidal.

Mazauna garin na Timbuktu dai sun nuna farin cikinsu a lokacin da sojojin Faransa da na Mali su ka shigo cikin garin.

Sai dai akwai wuraren da aka rika fasa shaguna da kuma gidajen jama'a ana satar kayan jama'a.

Har yanzu dai babu wutan latanki a garin na Timbukutu da kuma wayar salula.

Sai dai kafin 'yan tawayen su tsere daga garin, sun cinawa wasu gine-gine tarihi wuta dake dauke da wasu takardu masu dimbin tarihi.

Idan an jima a yau ne kasashen duniya za su gudanar da taro a Addis Ababa babban birnin Habasha don tara kudaden da za a yi amfani da su a yunkurin da ake yi na fatattakar masu tayar da kayar baya a arewacin na Mali.