'Shirin kafa sansanin jiragen Amurka a Nijar'

Shugaban Nijar yana duba faretin sojoji
Image caption Amurka na shirin amfani da sararin samaniyar Nijar

Rahotanni sun ce gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta baiwa Amurka izinin kafa wani sansani na jiragen da basu da matuka a Arewacin kasar.

Za kuma a dauki wannan mataki ne kamar yadda rahotannin su ka nuna domin tsaurara tsaro a wasu yankuna na arewa maso yammacin Afrika dake fama da matsalar ta'addanci.

Rahotannin sun ambato wani jami'in gwamnatin Nijar din daya nemi a saya sunansa, yana cewa Nijar din ta bada izinin ne a lokacin da Jakadiyar Amurka a kasar ta gaana da Shugaba Mahamadou Isufu a jiya.

Sai dai da BBC ta tuntubi ministan tsaron Nijar Alhaji Mahamadu Karijo kan wannan batu, ya shaida ma ta cewa ba shi da masaniya.

Wannan batu dai ya sa tuni wasu kungiyoyin farar hula a kasar su ka soma nuna damuwar su da kum a adawa da shirin gabakidayansa

Karin bayani