Gwamnatocin Najeriya zasu raba dala biliyan daya

Goodluck Jonathan na Najeriya
Image caption Za a raba dala biliyan guda tsakanin gwamnatocin Najeriya

A Najeriya, majalisar tattalin arzikin kasar ta amince da cire dala biliyan daya daga asusun rarar man kasar, domin rabawa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohin kasar talatin da shida da kuma Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

Majalisar tattalin arzikin kasar ta cimma wannan matsaya ne a yau, bayan da tai wani zama karkashin jagorancin mataimakin Shugaban kasar Arch. Namadi Sambo

Majalisar dai ba ta fito fili ta fayyace abin da gwamnatocin za su yi da wadannan kudade ba.

Sai dai a wata hira da BBC, Shugaban kungiyar Gwamnonin, kuma gwamnan jahar Rivers Rotimi Amechi yace ayyuakan raya kasa na daga cikin irin abubuwan da za a fi maida hankali akai wajen kashe wadannan kudade

A bara ne dai gwamnatin Najeriya ta kirkiri asusun kota- kwana, matakin da bai yiwa gwamnonin jahohin kasar dadi ba, abinda ya kai su ga garzayawa zuwa kotu.

Karin bayani