Wani attajiri a Afrika ta Kudu zai yi sadaka da rabin dukiyarsa

Patrice Motsepe
Image caption Motsepe ne bakar fata da ya fi kowa arziki a Afrika ta Kudu

Hamshakin ɗan kasuwan nan wanda shi ne baƙar fatar da ya fi kowa arziki a Afrika ta Kudu, Patrice Motsepe, zai sadakar da rabin abinda ya mallaka, inda zai yi koyi ga mutane biyun da suka fi kowa arziki a duniya Bill Gates da Warren Buffett.

Mr Motsepe, wanda ya mallaki fiye da dala biliyan biyu da rabi, zai zuba kudin ne a wani asusu domin tallafawa marasa galihu a Afrika ta Kudun.

Mai dakinsa, Precious Motsepe ta shaida wa BBC cewa lokacin ya yi da za su sauya yadda ake kallon nahiyar Afrika, sannan su nuna wa duniya cewa 'yan Afrika za su iya tallafawa kansu, maimakon a ce kullum sai an ba su agaji daga waje.

Fiye da attajirai 70 ne suka sanya hannu kan shirin na Bill Gates da Warren Buffett na ganin masu kudi sun bayar da rabin dukiyarsu sadaka.

Karin bayani