Zan dauki mataki kan shige da fice- Obama

Shugaban Amurka Barrack Obama ya ce lokaci yayi da za'a dauki matakai na bai daya da zasu tabbatar yin garanbawul a dokokin shige da fice a Amurka.

Mr Obama ya ce matukar 'yan Majalisar dokokin kasar basu dauki matakan da suka dace ba, shi da kansa zai gabatar da shawarwari da zai bukacesu su kada kuri'a akai.

Shugaban kasar ya kuma bayyana farin cikinsa game da shawarwarin da wasu 'yan majalisar dattawa da suka fito daga jam'iyu daban daban suka gabatar kan wannan batu.

Shugaba Obama ya ce mambobin dukkanin jam'iyu a Majalisun dokoki guda biyu suna aiki tare domin ganin an sami mafita.

A jiya dai wasu 'yan Majalisun suka sanar da shawarwarinsu dangane da yin garanbawul a dokokin shige da fice .

Shugaba Obama ya gabatar da shawarar karfafa tsaro ne a iyakokin kasar da kuma maida bakin haure sama miliyan goma sha daya 'yan kasa, kamar yadda wasu 'yan Majalisu suke nema a yi.