Za mu kulla sabon kawance da Algeria —Cameron

David Cameron
Image caption Firayim Minista David Cameron yayin ziyarar da ya kai Algeria

Firayim Ministan Birtaniya, wanda ke wata ziyarar aiki a Algeria, ya ce kasashen biyu sun amince su kulla wani sabon kawance da nufin kawar da barazanar mayakan sa kai masu tsattsauran ra’ayin addinin Musulunci a fadin Arewacin Afirka.

David Cameron ya furta wadannan kalamai ne bayan ganawar da ya yi da takwaran aikinsa na Algeria, Abdelmalek Sellal.

A cewarsa, “Dangane da kawancen da za mu so gani a tsakanin kasashen mu, tattaunawa a kan batun da ya shafi tsaro a tsakanin kasashenmu biyu abu ne mai muhimmanci.

“Mun tattauna yadda za mu kara zage dantse ta fuskar musayar ra’ayi a fannin tsaro da ma hadin gwiwa ta fuksar tsaron kasa da yaki da ta’addanci da kuma musayar bayanan sirri”.

Mista Cameron ya kuma ce wajibi kasahen duniya su yi duk wata mai yiwuwa don yakar ta’addanci.

Ya kuma ce garkuwar da aka yi kawanan baya da ’yan kasashen waje su 37 a Algeria manuniya ce cewa abin da ke faruwa a wadansu kasashe ka iya shafar sauran kasashen duniya.

Daga nan sai ya kare matakin da kasashen Yamma suka dauka na tsoma baki a rikicin kasar Mali.

Mista Cameron ne dai Firayim Ministan Birtaniya na farko da ya ziyarci kasar ta Algeria tun bayan samun mulkin kanta a 1962.

Karin bayani