An kai hare-hare a Najeriya cikin daren Laraba

Daya daga cikin hare-haren da aka kai a Kaduna, Najeriya
Image caption Daya daga cikin hare-haren da aka kai a Kaduna, Najeriya

Rahotanni daga Jihar Kaduna a arewacin Najeriya na bayyana cewa wadansu mutane da ba a san ko su wanene ba sun kai wani hari a cikin daren ranar Laraba (tsakanin karfe daya zuwa biyu na dare) a kan wani caji ofis a Birnin Gwari—sun kuma kona shi kurmus.

Mutanen da aka bayyana cewa suna da yawan gaske sun kuma fasa wadansu bankuna biyu ta hanyar amfani da manyan bindigogi.

Wakilin BBC a Kaduna ya bayyana cewa wadanda suka shaida faruwar al’amarin sun ce an yi ta ba-ta-kashi tsakanin maharani da jami’an tsaron da ke garin, wadanda ba yawa ne da su ba.

Ya kuma Ambato Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibrin Mai Gwari, yana cewa ranar Laraba suka je wajen gwamnan Jihar Kaduna suka kai kuka a kan a kara musu jami’an tsaro a garin.

Har yanzu dai ba a samu cikakken bayani a kan irin barnar da aka yi ba.

Daga Jihar Kano ma mai makwabtaka, rahotanni sun ce wadansu mutane wadanda kawo yanzu ba a tantance ko su wanene ba sun kona ofishin ’yan sanda a karamar hukumar Bunkure.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe Takwas na daren ranar Laraba.

Wani da ya ganewa idanuwansa faruwar al'amarin ya ce ya ga ofishin ’yan sandan na ci da wuta sannan ya ji karar fashewar wani abu.

Wadansu rahotannin da ba a tabbatar da ingancinsu ba sun ce al’amarin ya rutsa da wadansu mutane.

Kokarin da wakilin BBC a Kano ya yi na jin ta bakin rundunar ’yan sandan Jihar ta Kano ya ci tura saboda wayar kakakin rundunar tana ta kara ba a dauka ba.

Karin bayani