Gyaran tsarin mulkin Najeriya: An gamu da cikas a majalisa

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Ana yunkurin gyara kundin tsarin mulki a Najeriya

Majalisar wakilan Najeriya ta dage wani zaman da ta shirya don sanar da cikakken rahoton da ta hada a kan ra'ayoyin 'yan Najeriya game da gyaran-fuska ga kundin tsarin mulkin kasar.

Kakakin majalisar , Aminu Waziri Tambuwal ne ya sanar da dage zaman, amma bai fayyace dalilan dagewar ba.

Kungiyoyin farar-hula da wasu 'yan Najeriya da dama sun sha mamaki a wani zauren majalisar wakilan kasar bayan sun shafe kusan sa'a uku su na jiran tsammanin zuwan kakakin majalisar da mukarrabansa domin ya sanar da kammalallen rahoton ra'ayoyin 'yan kasar game da yin gyaran-fuska ga kundin tsarin mulkin Najeriya, ra'ayoyin da daidaikun 'yan majalisar suka karade mazabunsu yayin tattarawa.

Duk da cewa 'yan majalisar sun ki sakewa su fasa-kwai, binciken da wakilin BBC Ibrahim Isa ya yi ya nuna cewa Babban kundin ra'ayoyin da majalisar ta hada ne ke cike da abin da wasu su ka bayyana da kura-kurai, yayin da wasu kuma ke cewa wata makarkashiya aka shirya da nufin ha'intarsu, amma hakan ba ta cimma ruwa ba.

Bincike dai ya tabbatar da cewa an sassauya wa wasu 'yan majalisar ra'ayoyin al'umominsu, inda misali aka sanya wasu daga arewacin kasar cewa su na goyon bayan kirkirar sababbin jihohi, alhali ra'ayinsu na asali adawa suke yi da hakan.

Kazalika binciken ya gano cewa an sanya wa mafi rinjayen 'yan majalisar cewa mazabunsu suna goyon bayan a baiwa jihohi masu arzikin man kasar kashi ashirin bisa dari na kudaden shigar da ake samu daga mai, kuma wannan na daga cikin abin da ya sa 'yan majalisar ke cewa ba za ta sabu ba.

Karin bayani