Nigeria za ta kashe dala miliyan 40 a Mali

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin tallafa wa kasar Mali da sama da dala miliyon arba’in a yakin da ake yi da ’yan tawaye da kuma kokarin daidaita kasar a kan turbar dimokuradiyya.

Gwamnatin ta Najeriya t ace tuni ta tura sojoji 1,200 kasar Mali don taimakawa wajen kwato yankunan kasar da ’yan tawaye suka kame.

Ta kuma ce abin da za ta kasha wajen dawainiyar sojojin kadai da kuma ayyukan dakile ta’addanci a kasar ta Mali ya kai dala miliyan talatin da hudu (kwatankwacin naira miliyan dubu bakwai).

Baya ga wannan kuma, kamar yadda Shugaba Goodluck Jonathan ya sanar a wurin kaddamar da gidauniyar tallafa wa Mali—wanda aka yi a wajen taron kungiyar Tarayyar Afirka—Najeriya ta yi alkawarin tallafawa sojojin Mali da sauran dakarun da suka kai dauki kasar dad ala miliyan biyar.

Sai dai wadansu ’yan Najeriyar na ganin cewa wannan tallafi bai dace ba, saboda kasar tasu tana bayar da wannan agaji ne a daidai lokacin da wadansu ke ganin ita ma jami’an tsaronta na fama da rashin abubuwan more rayuwa a muhallansu, da kuma wuraren aikinsu.

Amma mai taimakawa shugaban kasar ta Najeriya a kan al’amuran yada labarai, Reuben Abati, ya ce shi bai ga wani abin korafi ba.

“Ya kamata mutane su fahimci cewa muna rayuwa ne a wata duniya da iyakokin da suka raba tsakanin kasashe suna ne kawai—duk abin da ya shafi wata kasa, to ya shafi sauran kasashe—saboda haka kasashenmu a hade suke”, inji Mista Abati.

Ya kuma kara da cewa: “Binciken jami’an liken asiri ya nuna cewa kasar Mali barauniyar hanya ce da ‘’yan ta’adda ke amfani da ita don shigowa da makamai Najeriya—ka ga idan aka dakile ayyuknasu a can tamkar an yi wa gida ne aiki”.

Karin bayani