Wani abu ya fashe a kamfanin mai na Mexico

Ma'aikatan ceto a ginin Pemex a Mexico
Image caption Ma'aikatan ceto na ci gaba da neman wadanda suka tsira a ginin Pemex a Mexico

Wani abu mai karfin gaske ya fashe a ginin hedkwatar katafaren kamfanin man fetur na gwamnatin kasar Mexico, wato Pemex.

Fashewar ta yi mummunan ta’adi ga bangaren gudanarwa na ginin kamfanin a arewacin Birnin Mexico.

Hotunan bidiyo sun nuna yadda baraguzai suka barbazu a kan titi a gaban ginin.

Wata mata ta kwatanta abin da ta gani:

“Na yi rauni a kafa saboda haka dole na tako a hankali na sauko daga hawa na ashirin da takwas. Abin da muka gani ya daga mana hankali matuka.

“Amma har yanzu ba mu san abin da ya faru ba”.

Ma'aikatan agaji da jiragen sama masu saukar ungulu da motocin daukar marasa lafiya na duba wadanda suka yi rauni.

Fashewar dai ta auku ne da misalin karfe hudu na yamma lokacin da ginin ke cike makil da ma'aikata.

Har yanzu babu wani bayani a hukumance a kan abin da ya haddasa fashewar, amma wadansu rahotanni na nuni da cewa matsalar wutar lantarki aka samu a ginin.

An yi amanna cewa mutane da dama sun makale a cikin baraguzan ginin, kuma ma'aikatan ceto na amfani da karnuka don sansano wuraren da mutanen suke a yunkurinsu na ceto wadanda suka tsira da rayukansu.

Ministan cikin gida na kasar, Miguel Angel Osorio, ya tabbatar da mutuwar akalla mutane goma sha hudu yayinda wasu tamanin suka jikkata, amma ana fargabar adadin wadanda abin ya rutsa da su zai karu.

Karin bayani