Najeriya: Tatsar bayanai a wayoyin mutane

Ginin hedkwatar hukumar sadarwa ta Najeriya
Image caption Ginin hedkwatar Hukumar Sadarwa ta Najeriya a Abuja

Hukumar Sadarwa ta Kasa a Najeriya, wato NCC, na shirin gabatar da wani kudurin doka a gaban Majilasar Dokoki, wadda za ta bayar da dama ga jami'an tsaro su tatsi bayanai daga wayoyin salula da e-mail da sauran hanyoyin sadarwa na jama'a.

Daya daga cikin hujjojin bullo da wannan doka ita ce samar da tsaro da taimakawa jami’an tsaro samun cikakkun bayanai.

A cewar kakakin hukumar ta NCC, yanzu haka an kafa wani kwamiti wanda ya kunshi masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa a Najeriya, kuma yana tattaunawa a kan wannan magana.

Sai dai wadansu ’yan Majalisar Dokokin sun ce bai kamata a rika sauraren hirarrakin jama'a ta wayar tarho ba tare da sanar da su ba.

Karin bayani