IMF ya yi kakkausar suka a kan Argentina

Shugabar Asusun IMF, Christine Lagarde
Image caption Shugabar Asusun IMF, Christine Lagarde

Argenatina ta zama kasa ta farko da Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, wato IMF, ya yi kakkausar suka a kanta saboda gazawa wajen bayar da alkaluma na kwarai dangane da tattalin arzikinta.

A wata sanarwa da ta fitar, hukumar gudanarwa ta Asusun ta ce Argentina ba ta dauki matakan gyaran da suka dace ba, don haka ba ta sauke wajibcin da ke kanta na kasancewa mamba a Asusun ba.

A cewar IMF, musamman alkaluman kasar a kan hauhawar farashin kayayyaki da arzikin da take samarwa a cikin gida ba sahihai ba ne.

A shekarar 2007 gwamnatin Argentina ta tsoma baki a harkokin cibiyar kididdiga ta kasar, kuma tun wancan lokacin masharhanta masu zaman kansu ke korafin cewa ba a bayyana wadansu daga cikin alkaluman.

Sai dai kasar ta Argentina ta sha fatali da duk wata suka a kan ingancin alkalumanta.

Ana dai ganin kakkausar sukar a matsayin matakin farko na kara daukar tsaurararan matakan da suka hada da kin baiwa kasar ta Argentina bashi ko ma korarta daga Asusun.

Karin bayani