Masar: Sabon tashin hankali a wajen Fadar Shugaban Kasa

zanga zanga a Masar
Image caption Taho mu gama tsakanin 'yan sanda da masu zanga zanga

Tashin hankali ya barke a Masar tsakananin masu zanga zangar kin jinin gwamnati da kuma 'yan sandan kwantar da tarzoma a wajen fadar Shugabancin Kasar dake birnin Alkahira

Masu zanga zangar sun yi ta jefawa jami'an tsaro manyan duwatsu da kuma bama baman da aka hada da fetur, wadanda su kuma su ka maida martani ta hanyar feshin ruwa da kuma harbi akan iska

Tashin hankalin na zuwa ne a yayinda dubun dubatar mutane su ka sake fita kan tituna a daukacin Kasar Masar domin yin Allawadai da Shugaba Mohammed Morsi.

A garin Port Said, masu zanga zangar sun kuma yi ta bayyana fushin su game da hukuncin kisar da aka yankewa wasu 'yan kwallo na wasan kwallon kafa su ashirin da daya game da mummunar zanga zangar da akai a bara

Karin bayani