Taho-mu-gama kusa da fadar shugaban Masar

Masu zanga-zanga suna harba bama-baman kwalba a kan fadar shugaban kasar Masar
Image caption Masu zanga-zanga suna harba bama-baman kwalba a kan fadar shugaban kasar Masar

Daruruwan masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Masar sun yi taho-mu-gama da dakarun tsaro a kusa da fadar shugaban kasar a birnin Alkahira.

Arangamar dai ta biyo bayan tashe-tashen hankulan da aka kwashe mako guda ana yi ne a kasar ta Masar wadanda suka jawo asarar rayuka kusan 60.

’Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da mesar ruwa don korar masu zanga-zangar wadanda ke jifa da duwatsu da bama-baman kwalba.

Gidan talabijin na Al-Hayat ya bayar da labarin cewa mutum guda ya rasa ransa, yayinda wasu fiye da hamsin suka jikkata.

Ma'aikatan agaji sun fito suna ta kokarin kula da wadanda suka jikkata:

Wata sanarwar da Shugaba Muhammad Morsi ya fitar ta ce jami’an tsaro za su dauki duk matakin da dace don kare gine-ginen gwamnati a birnin na Alkahira.

Sanarwar ta kuma ce fadar shugaban kasar za ta dora alhakin tashin-tashinar a kan ’yan siyasar da suka ingiza masu zanga-zangar.

Masu adawa da Shugaba Morsi ne dai suka yi kira da a gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a—duk da yarjejeniyar da bangarorin siyasar kasar, ciki har da kungiyoyin masu fafutuka da shugabannin majami'u, suka cimma ta yin Allah-wadai ta tashe-tashen hankula da kuma goyon bayan tattaunawa.

Bayan taron da aka cimma yarjejeniyar ranar Alhamis, daya daga cikin ’yan adawar, Mohamed El-Baradei, ya yi marhabin da ita:

“Muna da kyakkyawan fata daga wannan taro, amma fa har yanzu muna fuskantar kalubale da dama.

“Za mu yi iya bakin kokarinmu mu karfafa gwiwar Misrawa mu kuma sauya yanayin da Masar ke ciki”.

Masu zanga-zanar dai na zargin Shugaba Morsi ne da cin amanar juyin juya halin da suka yi shekaru biyu da suka gabata.

Amma magoya bayansa sun ce abin da ke faruwa wani yunkuri ne na kifar da gwamnatin shugaban kasar na farko da aka zaba a bisa tsarin dimokuradiyya.

Karin bayani