Kotu ta ce a tsare Faruk Lawan a kurkuku

Hon Faruk Lawan
Image caption Dan majalisar ya musanta cewa ya aikata laifi.

Wata kotu a Najeriya ta bada umarnin a tsare dan majalisar wakilan kasar Faruk Lawan a jarum, bisa zargin da ake masa na karbar cin hanci da rashawa.

Gwamnatin Nigeriya ce ta gurfanar da Hon Farouk Lawan wanda shi ne tsohon shugaban kwamitin wucin gadi na Majalisar wakilan kasar wanda aka dora wa alhakin gudanar da bincike kan sama da fadin da ake zargin an yi da kudaden tallafin man fetur a kasar.

An gurfanar da shi ne tare da sakataren kwamitin, Mr Emenalo Boniface.

Gwamnatin na tuhumar mutanen biyu ne da karban cin hanci daga wurin hamshakin dan kasuwar nan Femi Otedola da yawansu ya kai dala dubu dari shida da shirin domin cire sunan kamfaninsa daga jerin sunayen kamfanonin da kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai ya samu da laifi a binciken da yake yi game da talafin man fetur.

Sai dai wasu masu sharhi na ganin gwamnatin kasar ta gurfanar da mutanen biyu ne a gaban shari'a bayan matsin lambar da kuma barazanar da wasu lauyoyi masu fafutuka suka rika yi akan cewa za su dauki matakin shigar da kara da kansu idan gwamnati ba ta yi komai gameda lamarin ba.

Beli

Daya daga cikin lauyoyin kasar Festus Keyamo ya debar wa gwamnati wa'adin kwanakin bakwai kuma a ranar ashirin da tara na watan Janairun daya gabata ne wa'adin ya zo karshe.

Gwamnatin Najeriya ta ce an samu jinkiri wajen hukunta dan majalisar ne, saboda shari'a ce dake bukatar a yi bincike yadda ya kamata kafin a fara ta, kamar yadda lauyan ma'aikatar shari'a ta kasar Barista Adeboyega Awomolo ya shaida wa 'yan jarida a harabar kotun.

"Ku fada wa 'yan Najeriya da kuma duniya bakidaya cewa gwamnatin Najeriya ta damu gameda matsalar rashawa a kasar kuma wannan shari'a ce dake bukatar a yi bincike yadda ya kamata da kuma kwarewa daga wurin masu shigar da kara kuma ina bada tabbacin cewa abinda za'a gani kenan." In ji lauya Awomolo

Shi kuwa a dayan bangaren Barista Ricky Tarfa daya daga cikin lauyoyin dake kare Farouk Lawan cewa yayi, sun nemi kotu ta basu belinsa, amma kotun ta sanya ranar takwas ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za ta yanke hukunci gameda bukatar da suka shigar a gabanta.

Kotun a yanzu ta bada umurnin a je a tsare su a gidan kurkuku har zuwa ranar 8 ga watan Fabrairu lokacin da za ta yanke hukuncin game da belin.

Musanta wa

'Yan Najeriya da dama sun yi mamaki a lokacin da aka ce ana zargin Faruk Lawan da karbar rashawa, domin a lokacin da ya ke jagorantar kwamitin binciken kudaden tallafin man fetur, da yawansu na yi masa kallon mutum ne mai gaskiya da rikon amana.

Hakan ya sa aka yi ta cece-kuce a lokacin da aka dauki lokaci mai tsawo ba tare da an yi masa shari'a ba.

Shi dai dan majalisar Faruk Lawan, ya sha musanta zargin cewa ya aikata cin hanci da rashawa.

A karkashin dokokin Najeriya dai, da wanda ya karbi rashawa da wanda ya bayar duk suna da laifi, hakan ya sa wasu 'yan kasar ke mamakin ko me ya sa ba a gurfanar da hamshakin dan kasuwar nan Femi Otedola tare da su ba, tunda shi ake zargi da bada cin hancin?

Karin bayani