François Hollande zai je Timbuktu yau Asabar

Shugaba Francois Hollande na Faransa
Image caption Shugaba Francois Hollande na Faransa zai kai ziyara Timbuktu

Ana sa ran yau Asabar Shugaba François Hollande na Faransa zai kai ziyara birnin Timbuktu na arewacin Mali, kwanaki kadan bayan da dakarun kasarsa da sojojin Mali suka karbe iko da manyan garuruwan arewacin daga hannun 'yan tawaye.

Wakilin BBC da ke yankin ya ce Mista Hollande yana sa ran samun kyakkyawar tarba, tun da hankalin al'ummar Timbuktu ya kwanta kasancewar ’yan tawaye sun bar garin.

Ana sa ran Mista Hollande zai bukaci dakarun sojin Yammacin Afirka su kara kaimi, ita kuma gwamnatin rikon kwaryar Mali ta maido da tsarin dimokuradiyya cikin gaggawa, ta kuma tuntubi kungiyoyin ’yan adawa a arewacin kasar.

A halin da ake ciki kuma Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa akwai fargabar kai harin ramuwar gayya a kan Azbinawa da Larabawa a arewacin kasar ta Mali, a garuruwan da dakarun sojin Faransa da sojojin Mali suka sake karbe iko.

Jami’an Majalisar ta Dinkin Duniya sun ce akwai zargin cin zarafin jama’a da sojojin Mali ke aikatawa.

Sun kuma ce wani gungun jama'a sun kai hari a kan Azbinawa da Larabawa da kuma dukiyoyinsu.

Karin bayani