Mutum 32 sun hallaka a kamfanin mai na Mexico

Kamfanin Pemex
Image caption An sami asarar rayuka bayan fashewar wani abu

Shugaban Kamfanin mai na Kasar Mexico Pemex yace akalla mutane talatin da biyu ne su ka mutu, fiye da dari kuma sun samu raunuka bayan fashewar wani abu da ya girgiza hedikwatar kamfanin a birnin Mexico

Emilio Lozoya yace ya yi wuri a gano abinda ya janyo fashewar abin

Shugaban kasar Enrique Pena Nieto ya yi alkawarin cewa za'a gudanar da cikakken binciken fashewar wadda ta auku a wani gini dake daura da kamfanin a lokacin da ma'aikata suke sauyin aiki.

Jami'ai sun ce har yanzu akwai mutane kusan talatin wadanda suke makalle a dogon ginin.

Kasan ginin ya yi kaca-kaca kuma wadanda suka tsira sun ce ginin ya girgiza kwarai. Wakilin BBC a Mexico yace wannan shine fashewar abubuwa masu karfi da aka fuskanta a birnin a tsawon shekaru talatin da suka gabata.

Karin bayani