Salman Khan ya fuskanci tuhumar aikata kisa

Image caption Salman Khan, jarumin fina-finan India

Wata kotun India ta tuhumi fitaccen jarumin fina-finan India, Salman Khan da aikata bayan ya kaɗe wani mutu da mota shekaru goma da suka gabata.

Cikin watan Satumbar sheara ta 2002 ne aka zargi jarumin da tuƙin ganganci da ya kai ga aukawa wani gidan biredi a birnin Mumbai.

Kuma lamarin ya haddasa mutuwar wani maras galihu dake kwana a bakin titi.

Idan dai har kotu ta same shi laifin jarumin zai iya fuskantar zaman gidan yari na shekaru goma.

Sai dai kuma ya musanta zargin.

Salman Khan dai fitaccen jarumi ne mai farin jini a a fina-finan India, inda ya fita fina-finai fiye da tamanin da suka shahara.