Cameron zai gana da Karzai, Zardari

Hamid Karzai, da David Cameron, da Asif Ali Zardari
Image caption Shugaba Karzai, da Firayim Minista Cameron, da Shugaba Zardari a New York bara

Da maraicen ranar Lahadi ne ake sa ran Firayim Ministan Birtaniya, David Cameron, zai fara wata tattaunawa ta kwanaki biyu da shugabannin Afghanistan da Pakistan da nufin karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen da kuma tallafawa yunkurin samar da zaman lafiya da sasantawa a Afghanistan.

Firayim Ministan na Birtaniya zai karbi bakuncin Hamid Karzai da Asif Ali Zardari ne yayin wani bikin cin abincin dare, kafin tattaunawar da za a yi ranar Litinin a wani bangare na matakin sasanatawar da Mista Cameron ya assasa bara.

Ofishin Firayim Ministan na Birtaniya na Downing Street ya ce yana sa ran tattaunawar za ta mayar da hanakali a kan shirin samar da zaman lafiya a karkashin jagorancin ’yan Afghanistan, da kuma yadda Pakistan da sauran kasahen duniya za su iya tallawa shirin.

Kawar da rashin yarda da juna a tsakanin makwabtan biyu dai batu ne mai matukar muhimmanci.

Gwamnatin Afghanistan ta bayyana karara cewa tana kallon sakin ’yan Taliban da Pakistan ta yi kwanan nan a matsayin wani mataki mai kyau, amma kuma tana so a saki mutum na biyu mafi girman mukami a kungiyar ta Taliban, Mullah Baradar.

Fatanta shi ne cewa mutum mai matsayinsa zai iya shawo kan ’yan Taliban din su hau teburin shawarwari da gwamnatin.

A karo na farko jami’an soji da na leken asiri daga kasashen biyu za su shiga wannan tattaunawa, kuma jami’ai sun yi amanna hakan zai taimaka wajen tunkarar wadansu daga cikin muhimman batutuwa a yunkurin na sasantawa.

Ba makawa karatowar wa’adin janye dakarun kungiyar tsaro ta NATO daga Afghanistan ya zama wani muhimmin batu a tattaunawar, musamman ma saboda damuwar da Pakistan ke nunawa dangane da tsaro a fadin yankin bayan janyewar.

Karin bayani