An jinjinawa Shugaban Faransa a Timbuktu

Shugaba Francois Hollande na Timbuktu
Image caption Francois Hollande ya samu tarba ta musamman a garin Timbuktu

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande wanda ya kai ziyara Mali domin jinjinawa kwazon sojojin Faransa bisa nasarar da su ka samu ta fatattakar yan tawayen Ansarudeen ya ce an kora ayyukan ta'addanci baya a Mali, amma ba'a kammala shawo kansa ba tukunna.

A jawabin da ya yiwa cincirindon jama'a a Bamako baban birnin kasar Mali Mr Hollande ya yi kira a martaba dukkanin hakkokin dan Adam ko da kuwa 'yan tawaye ne.

Da yake jawabi a birnin Timbuktu Mr Holland yace sojin Faransa za su tsaya a Mali har zuwa lokacin da sojojin Afirka da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya za su isa can.

Jama'a da dama dai a Malin sun yi marhabin da zuwan Shugaban Fransan Kasar Faransa, sai dai masharhanta na ganin cewar har yanzu akwai jan aiki a gaban sojojin da dakarun Kasar Faransan ke jagoranta a Malin.

Karin bayani