An karya 'yan ta'adda, amma... —Hollande

Shugaba François Hollande na Faransa
Image caption Shugaba François Hollande na Faransa ya ziyarci Timbuktu

Shugaba François Hollande na Faransa ya ce an ci karfin ta'addanci a Mali, amma ba a gama da shi ba baki daya tukuna.

A jawabin da ya yi yayin wani taron manema labarai da suka kira shi da shugaban gwamnatin rikon kwarya ta Mali, Dioncounda Traore, François Hollande ya ce ko da yake an karya lagon 'yan tawayen, da sauran aiki a gaba:

“Yakin bai kare ba tukuna. An raunana kungiyoyin ’yan ta’adda, an haddasa musu mummunar asara, amma fa ba a gama da su ba”.

Shugaban na Faransa ya kuma yi kira da a mutunta ’yancin dan-Adam na kowa har ma da masu ta-da-kayar-baya.

Kafin nan, da yake jawabi a Timbuktu, Mista Hollande ya ce dakarun Faransa za su ci gaba da kasancewa a Mali har zuwa lokacin da rundunar kasashen Afirka mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya za ta karbi ragamar kare kasar.

“Ina so in shaidawa mutanen Mali masu son zuwa wurina su yiwa Faransa godiya cewa ba mu kammala abin da ya kawo mu ba tukuna, lallai za mu ci gaba da dannawa tun da ba a kammala ’yanta daukacin kasar Mali ba”, inji Mista Hollande.

Ya kuma kara da cewa: “Za mu kasance tare da al'ummar Mali da al'ummar Afirka, ciki har da wadanda ke arewacin Mali, har sai mun fatattaki kungiyoyin ’yan ta'adda”.

Da yake nasa jawabin, Mista Traore ya godewa Faransa da al'ummarta saboda aikewa da dakaru don a yaki masu ta-da-kayar-bayan.

Jama’ar da suka taru a wurin sun yi ta sowa lokacin da Mista Traore ke ambato sunayen garuruwa da biranen kasar da aka kwato daga hannun 'yan tawayen.

Wadansu ’yan siyasar Faransa dai sun bayyana fargabar cewa zaman dakarun Faransa a Mali ka iya zarta wa’adin da Shugaba Hollande ke diba, saboda dakarun kasar da na kasashen Afirka ba su shirya tabbatar da tsaro ba.

Karin bayani